Akalla gwamnonin Arewa 11 suka yi wani zama dan fitar da mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC

0 66

Akalla gwamnonin arewa ne 11 suka yi wani zama da dan takarar shugabankasa na jam’iyyar APC .

Taron wanda akayi da nufin zakulo wanda zai yi takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023.

A matsayinsa na dan kudancin kasar nan ana sa ran zai dauki wanda zai masa mataimaki daga arewa.

 kakakin kwamatin yakin neman zaben Tinubu Bayo Onanuga, ya gayawa manema labarai cewa, gwamanoni ne ke da ta cewa kan wanda zai yiwa jam’iyyar APC mataimakin shugaban kasa a zaben da za’a gudanar a badi.

Hakumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bawa jam’iyyun siyasa wa’adin mako guda su mika sunayen wanda zasuyi takarar mataimakan shugaban kasa na jam’iyyunsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: