Akalla kauyuka 11 ne ambaliyar ruwa ta mamaye a karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa

0 110

Akalla kauyuka 11 ne ambaliyar ruwa ta mamaye a karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa.

Shugaban karamar hukumar, Shehu Sule Udi ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Ringim.

Ya ce ambaliyar ruwan ta yi barna tare da raba mutane da muhallansu, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, tare da lalata daruruwan gidaje da filayen noma da sauran dukiyoyi sakamakon ambaliyar da madatsar ruwa ta Tiga ta yi.

Sule Udi ya ce karamar hukumar ta kwashe wadanda abin ya shafa tare da mayar da su sansanonin ‘yan gudun hijira a garuruwan Ringim da Gerawa.

Ya ce karamar hukumar ta kuma ba su abinci da ruwan sha mai kyau da magunguna.

Shugaban karamar hukumar ya bukaci jihar da gwamnatocin tarayya da sauran daidaikun jama’a da su gaggauta kai dauki ga wadanda abin ya shafa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: