Akalla masu sana’ar gwangwan 55 ne suka rasa rayukansu a jerin hare-haren da mayakan Boko Haram suka kitsa a jihar Borno

0 75

Akalla masu sana’ar gwangwan 55 ne suka rasa rayukansu a jerin hare-haren da mayakan Boko Haram suka kitsa a cikin makonni uku da suka gabata a jihar Borno.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abdu Umar ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a wajen taron masu ruwa da tsaki na tsaro a birnin Maiduguri.

Masu ruwa da tsakin sun hada da ‘yan sanda, sojoji, jami’an tsaron farin kaya da hukumar tsaro ta jihar da dai sauransu.

Taron wanda aka shirya da nufin tattaunawa tare da samar da mafita kan hare-haren da ake kaiwa Yan gwan-gwan a jihar.

Umar ya ce ‘yan ta’addan sun kashe Yan gwan-gwan 32 a kauyen Modu da ke karamar hukumar Kala-Balge, yayinda aka kashe wasu 23 a kauyen Mukdala na karamar hukumar Dikwa

Ya ce wadanda lamarin ya rutsa da su sun kutsa cikin dazuzzukan da ke da tazarar kilomita 25 daga garuruwan ba tare da sanar da jami’an tsaro ba.

Sai dai, Umar Usman, wanda shine shugaban kungiyar Yan gwan-gwan ta jihar, ya ce wadanda harin Kala-Balge da Dikwa ya shafa ba Yan kungiyarsu ba ne, saboda basu da rijista a hakumance.

Leave a Reply

%d bloggers like this: