Akalla mata masu juna biyu 25 ne suka haifi sabbin jarirai a sansanin ‘yan gudun hijira na Karnaya da ke karamar hukumar Dutse a jihar Jigawa

0 69

Akalla mata masu juna biyu 25 ne suka haifi sabbin jarirai a sansanin ‘yan gudun hijira na Karnaya da ke karamar hukumar Dutse a jihar Jigawa.

Rahotanni sun nuna cewa jariran da aka haifa a cikin kasa da makonni biyu ba’a yi musu rigakafin kamuwa da cututtukan da ke kashe kananan yara ba.

Kauyen Karnaya mai tazarar kilomita 23 daga Dutse babban birnin jihar Jigawa, na daya daga cikin kauyukan da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Jigawa.

A lokacin da ‘yan jarida suka ziyarci sansanin ‘yan gudun hijirar, an rawaito cewa matan 25 sun haihu a cikin makonni biyu da komawarsu ba tare da wata kwararriyar ma’aikaciyar haihuwa ba.

Da yake zantawa da manema labarai, shugaban sansanin ‘yan gudun hijira na cikin gida, Malam Falalu Ado, ya ce mata na haihuwa a sansanin ba tare da kulawar kwararrun likitoci ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: