Akalla mutane 24 ne suka mutu sanadiyyar wani gini da ya ruguje a ƙasar Afrika ta Kudu

0 140

Hukumomi a kasar Afrika ta Kudu sun ce adadin wadanda suka mutu sanadiyyar wani gini da ya ruguje a yau Litinin a birnin George da ke kudancin ƙasar sun kai 24.

Har yanzu kuma ana ci gaba da kokarin ceto tare da kwaso gawarwakin wasu mutane 28 da suka makale a karkashin baraguzan ginin.

Mutane 81 ne ke cikin ginin mai hawa biyar a lokacin da ya ruguje.

Daga cikin su mutane 29 ne da suka tsira, 13 na kwance a asibiti.

Ana dai binciken musabbabin rugujewar ginin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: