Akalla mutane 2968 aka kashe yayin da aka sace 1484 a Najeriya daga watan Janairu zuwa Maris na bana

0 38

Akalla mutane dubu 2 da 968 aka kashe yayin da aka sace dubu 1 da 484 a Najeriya daga watan Janairu zuwa Maris na bana, kamar yadda bayanan wata kungiyar tsaro a Najeriya ya nuna.

Bayanai sun ce an kashe mutane da dama a yankin Arewa maso Yamma fiye da sauran yankunan kasar. Akalla mutane dubu 1 da 103 ne aka kashe a cikin watannin a yankin.

Yankin Arewa ta Tsakiya ya kasance na biyu a yawan kashe-kashe inda aka kashe mutane 984 a watannin, yayin da a Arewa maso Gabas aka kashe mutanen 488.

A yankin Kudu-maso-Gabas an kashe mutane 181 cikin watannin, yayin da a yankin Kudu maso Yamma aka kashe mutane 127, inda aka kashe 85 a yankin Kudu-maso-Kudu cikin watannin.

Bayanai sun nuna cewa a yankin Arewa-maso-Yamma an yi garkuwa da mutane 746 cikin watannin. A yankin Arewa ta tsakiya an sace mutane 547 yayin da aka yi garkuwa da mutane 61 a yankin Arewa maso Gabas cikin watannin.

A yankin Kudu maso Gabas, an sace mutane 53, inda aka sace mutane 44 a Kudu maso Kudu sannan kuma an sace mutane 36 a Kudu maso Yamma cikin watannin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: