Akalla mutane 84 suka mutu kuma gommai suka jikkata bayan fashewar wata babbar tankar a kasar Saliyo

0 77

Akalla mutane 84 suka mutu kuma gommai suka jikkata bayan fashewar wata babbar tankar mai a Freetown, babban birnin kasar Saliyo.

Fashewar ta auku ne da yammacin jiya Juma’a, bayan da wata motar dakon mai ta yi karo da wata motar.

Hotunan da kafafen yada labaran kasar suka yadawa sun nuna gawarwakin da suka kone a kan titunan da ke kewaye da tankar.

Shugaban kasar Julius Maada Bio ya ce ya damu matuka da mumunar fashewar da kuma asarar rayuka da aka yi.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter, ya ce gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa domin tallafawa iyalan wadanda abin ya shafa.

Magajin garin birnin Freetown ya bayyana al’amarin a matsayin mai muni inda ya ce ba a san yawan adadin wadanda abin ya shafa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: