Akalla mutane bakwai ne suka rasa rayukan su, yayin da dama suka jikkata a wasu hare-hare guda biyu da aka kai a Karmar hukumar Damboa dake jihar Borno.
A harin farko da aka kaddamar, yan ta’addan sun kai hari ne ga manoma a gonakin su, inda suka hallaka biyar daga ciki tare da barin da dama daga cikin manoma da munanan raunuka.
Wata majiya daga wani jami’in sa kai, ya shaidawa manema labarai cewa jami’an soji sun gano gawarwakin wadanda lamarin a yamacin ranar bayan samun bayanan kai harin.
Ana sa ran za’a binne mamatan a yau kamar yadda addinin musulunci ya tanada.