Labarai

Akalla mutane biyar ne suka mutu bayan da aka yi ruwan sama tare da iska mai karfi wacce ta yi barna a Damaturu na jihar Yobe

Akalla mutane biyar ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata, bayan da aka yi ruwan sama tare da iska mai karfi wacce ta yi barna a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

An rawaito cewa lamarin ya kuma lalata gidaje sama da 100.

Babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Yobe, Mohammed Goje, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar jiya.

Ya ce tawagar hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Yobe a jiya, sun amsa kiran gaggawa da wasu mutane nagari suka yi, tare da tallafa musu wajen kwashe wadanda abin ya shafa zuwa asibitin kwararru na jihar Yobe.

Mohammed Goje ya kara da cewa mutanen 41 da lamarin ya shafa, biyar daga cikinsu sun mutu, kuma sun fito ne daga al’ummomi da wurare daban-daban guda 6 a babban birnin jihar sannan an kai su asibiti.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: