Akalla mutum 6 sun mutu kuma wasu dayawa suka jikkata a wani harin kunar bakin wake a Mogadishu, babban birnin kasar Somalia

0 147

Ma’aikatan ceto a kasar Somalia sun ce akalla mutane 6 ne suka mutu kuma wasu dayawa suka jikkata a wani harin kunar bakin wake a Mogadishu babban birnin kasar.

Kungiyar masu da’awar jihadi ta al-Shababa ta dauki alhakin kai harin.

Kakakin kungiyar, Abdiasis Abu Musab, yace dan kunar bakin waken ya nufi wata karamar motar bus cike da masu zabe wadanda ke zaben ‘yan majalisar dokokin kasar.

Dayawa daga cikin wadanda suka mutu masu tafiya a kafa ne a gefen titi.

Ana cigaba da samun yawaitar hare-hare cikin ‘yan makonninnan daidai lokacin da ‘yan siyasa ke kokarin samun damar zaman ‘yan majalisa domin zabar sabuwar gwamnati da shugaban kasa.

Masu sharhi kan harkokin tsaro sun ce ‘yan siyasa na bangaren adawa ne suka kitsa mafiya yawan hare-haren, wasu ta hanyar kungiyar al-Shabab, wadanda mayakansu ke aiwatar da kashe-kashe a madadinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: