Akalla mutum 8 ne suka mutu tare da jikkata wasu biyu a wani hatsarin mota a jihar Filato

0 93

Akalla mutum 8 ne suka mutu tare da jikkata wasu biyu a wani hatsarin mota a jihar Filato.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a jiya, jami’in wayar da kan jama’a na hukumar kiyaye haddura ta jihar, Peter Longsan, ya ce hatsarin ya afku ne a hanyar Jos zuwa Lamingo a jiya.

Lamarin dai ya faru ne sakamakon gudun wuce sa’a da direbobin motar sukeyi, lamarin da yasa motocin biyu suka ci karo.

Longsan ya shawarci masu ababen hawa da su kiyaye gudu, yana mai nuni da cewa gudun wuce kima ke haddasa mafi yawan mace-mace da munanan raunuka akan hanyoyin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: