Akalla sojoji 24 ne suka mutu a harin da ake zargin ƴan bindiga ne suka kai a Jamhuriyar Nijar

0 97

Sojojin da suka mutu a harin da ake zargin ƴan bindiga ne suka kai a kan jami’an tsaro a yankin Yammacin Tillaberi na Jamhuriyar Nijar a ranar 27 ga Agusta sun haura zuwa 24, kamar yadda kafar watsa labaran tsaron Kasar ta bayyana.

Amma daga baya da sojojin ƙasar suka kai ɗauki, sun sake gano wasu gawarwakin guda 17, inda jimilla ta zama 24.

Bayan haka kuma akwai gomman sojoji da har yanzu babu labarinsu, kamar yadda rahoton ya nuna a shafin X. Wannan harin na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban sojin ƙasar, waɗanda suka karɓe mulki bayan hamɓarar da Mohamed Bazoum ke cigaba da yaƙi da ƙungiyoyi ƴan bindiga masu iƙirarin jihadi, musamman masu alaƙa da al-Qaeda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: