Akalla yara 38 ne suka kamu da cutar Polio a kananan hukumomi 12 dake jihar Bauchi

0 60

Akalla yara 38 ne suka kamu da cutar Polio a Kananan Hukumomi 12 dake jihar Bauchi kamar yanda hukumar lafiya matakin farko ta jihar ta bayyana.

Shugaban hukumar Dr Rilwanu Mohammed ne ya bayyana hakan a lokacin da suke kaddamar allurar rigakafin cutar a unguwar Bayan Fada dake Bauchi.

A cewar Muhammad ansamu sabbin mutanen ne a kananan hukumomin Toro, Warji, Darazo, Misau, Dambam, Zaki, Jamaare, Alkaleri, Ganjuwa, Bauchi, Katagum da kuma Shira.

A cewarsa yanzu haka hukumar su ta karbi sabbin alluarar rigakafin cutar.

Ya kuma ce mutanen da zasu karbi wannan allaurar rigakafin yara ne yan kasa da shekara 5 wadanda yawansu ya kai miliyan 2,286,057.

Akwai kuma rigakafin da yawansa ya kai miliyan 2,367,450 a wajen hukumar su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: