Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya amince da cewa miliyoyin ‘yan Najeriya na fama da bakin talauci.
Yace shugabannin da aka zaba a yanzu, zasu zama na jeka na yi ka matukar basu hada kai ba wajen magance abinda da ya kira matsalolin dake neman tarwatsa kasarnan ba.
Osinbajo ya fadi hakan ne yayin bikin rufe taron wuni biyu tsakanin bangaren zartarwa da majalisa wanda aka gudanar a fadar shugaban kasa dake Abuja.
- Gwamna Otu Ya Fadi Abubuwan da ke Janye Gwamnoni zuwa jam’iyar APC
- Atiku Abubakar yayi magana kan ficewar sa daga PDP
- Hukumar NEMA ta karɓi ‘yan Najeriya 203 da aka kwaso daga kasar Libya
- Kwamiti na jam’iyyar PDP ta yanke shawarar daukar matakin shari’a kan Sheriff Oborevwori
- Hukumar NDLEA ta yi nasarar kama kwayoyin da kudinsu ya haura naira biliyan 2.6 a Jihar Jigawa
Yace akwai bukatar yan bangaren zartarwa da yan majalisa su hada kai muddin suna gudun bawa yan Najeriya kunya, wadanda suka basu damar rike mukaman siyasa a manyan matakai.
A takardar bayan taro da aka fitar a karshe taron, wadanda suka halarci taron, sun nemi a samar da shiri mai inganci na sansanta juna tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa, domin cigaban kasa.