Akwai tsananin matsalar karancin malaman makaranta a jihar Jigawa, a cewar Shugaban Kungiyar Malaman Makaranta

0 133

A wani bincike da jaridar Daily Trust ta buga ranar Asabar, ta gano cewa sabanin wasu jihohin a Najeriya da ke fama da matsalar kasa biyan malaman makaranta albashinsu, jihohin Kano, Jigawa, Katsina, Lagos, Ekiti da ma wasu jihohin gwamnatoci na cika alkawuran da suka dauka na biyan malamai hakkinsu.

Malaman makaranta da kuma wakilan gwamnati a jihohin sun bayyanawa Daily Trust cewa, ana biyan albashin malaman akan lokaci.

Jami’in Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Malam Aliyu Yusuf ya ce, gwamnatin jihar Kano tana samun nasara wajen biyan albashin malamai yanda ya kamata.

Ya kara da cewa, matsala daya da ake fuskanta ita ce rashin samun damar ciyar da malamai gaba promotion matsalar da gwamnatin ta gada daga gwamnatin baya, amma kuma ya ce, gwamnati ta san da matsalar, kuma kwanannan za a gyara komai.

Wata majiya daga ma’aikatar ilimi ta ce, Gwamna Abdullahi Ganduje da shi da shugabannin kananan hukumomi sun zama daya wajen tabbatar da gudanar kudaden albashin malaman.

“Kun san cewa, kananan hukumomi suna bayara da wani kaso don biyan albashin bayan wanda yake zuwa daga gwamnatin tarayya. A Kano kuma, gwamna ya tabbatar da cewa albashin malaman makaranta shine farko kafin saura.”

A jihar Jigawa kuma, Kungiyar Malaman Makaranta NUT reshen jihar ta yabawa gwamnatin jihar wajen biyan malamai albashinsu da sauran hakkokinsu a kan lokaci.

Shugaban Kungiyar, Abdulkadir Yunusa ne ya tabbatar da hakan a wata hira da Daily Trust a ranar Asabar, inda ya kara da cewa akwai tsananin matsalar karancin malaman makaranta a jihar.

Da yake kara tabbatar da matsalar malaman makaranta a jihar, kwamishinan ilimi, kimiyya da fasaha a jihar, Dr. Lawan Yunusa Danzomo, ya ce an mayar da hankali wajen magance matsalar karancin malaman makarantar.

Kwamishinan ya kara da cewa, jihar Jigawa na da adadin malaman makaranta 15,800 gaba daya a fadin jihar.

Ya kara da cewa, gwamnatin jihar ta debe malaman makaranta 6,500 a kwanannan, wadanda suka hada da 1,900 a matsayin cikakkun malaman makaranta da kuma 4,500 a karkashin shirin J-Teach.

Leave a Reply

%d bloggers like this: