Akwai Yiwuwar A Zubar Da Wasu Zaɓaɓɓun Ministoci A Kwandon Shara -In Ji Sanata Lawrence

0 319

Sanata Lawrence Ewurudjiako daga Jihar Bayelsa, ya yi ƙarin hasken cewa duk sabon ministan da bai damka takardar rantsuwar yawan kadarorin da ya mallaka ba, to ba za’a amince da naɗin sa ba.

Sanata Lawrence ya yi wannan bayanin ne a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai a Majalisar Tarayya. Lawrence ya kara da cewa tun a cikin majalisa ya gabatar da hanzarin bayan kammala tantance tsohon ministan harkokin sufurin jiragen ƙasa, Hadi Sirika.Sirika na daya daga cikin ministoci 43 da Shugaba Muhammadu Buhari ya nada, kuma ya mika sunayen su a majalisar Dattawa.

An umarci Sirika ya yi wa majalisar ruku’un al’ada ya fice, a bisa alfarmar ya taba yin dan majalisa. Hakan ya sa ba a yi masa tambayoyi ba.

Bayan Sirika ya fice ne sai Sanata Lawrence ya ja hankalin majalisa a kan batun takardun rantsuwar duniyar da mutum ya mallaka, wato ‘asset declaration’.

Ya ce wasu ministocin da ake tantancewa din ba su hado da takardun rantsuwar dukiyar da suka mallaka ba.Ya ce dokar kasa ta bada umarni cewa kama daga Shugaban kasa da Mataimakin sa da shugabannin tsaron soji da ministoci sai sun gabatar da takardun su na yawan dukiyar da suka mallaka.

Ya ce ya lura wasu babu satifiket din suka kawo takardun su, kuma wannan ba daidai ba ne.

Leave a Reply

%d bloggers like this: