Akwai yiwuwar jefa ƴan Najeriya cikin duhu matuƙar gwamnati bata biya bashin Naira Triliyan huɗu ba

0 108

Kamfanonin rarraba lantarki na kasar nan sun yi barazanar jefa ƴan ƙasar cikin duhu matuƙar gwamnati bata biya su bashin da suke binta na naira Triliyan huɗu ba.

Ta cikin wata sanarwa da shugaban gamayyar kamfanonin Kanal Sani Bello mai ritaya ya rarrabawa manema labarai, ta ce ya zama dole ta ɗauki matakin tilastawa gwamnati ta biya su bashin, don magance wasu manyan matsaloli da kamfanonin ke fama da su sakamakon rashin kuɗi.

Wannan matakin na zuwa ne a dai-dai lokacin da gwamnati ta ke shirin haramta shigar da farantan da ke adana hasken wutar lantarki zuwa ƙasar nan, matakin da ya fara jefa fargaba a zukatan ƴan ƙasa da basu da tabbas kan samuwar wutar lantarki.

A cewar ƙungiyar kamfanonin, tsadar sauyin kuɗaɗen ƙasashen ƙetare, da yadda ake tilasta musu biyan wasu haraje-haraje da dala na ɗaya daga cikin abinda ke ƙara jefa su cikin matsaloli na kuɗi.

Matakin na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan da gwamnati ta ci tarar kamfanonin maƙudan kuɗaɗe a sakamakon arigizon kuɗin wuta da suke yiwa jama’a.

Leave a Reply