Akwai yiwuwar za a samu ruwan sama mai karfin gaske a jihohin Katsina da Jigawa da Neja da Kogi

0 129

Hukumar kula da yanayi ta kasa tace cikin kwanaki uku masu zuwa, akwai yiwuwar za a samu ruwan sama mai karfin gaske a jihohin Katsina da Jigawa da Neja da Kogi da Nasarawa da Benue da Cross River.

Hukumar ta bayyana cewa akwai yiwuwar a fuskanci matsakaicin ruwan sama ko mai yawa a wasu yankunan Jihohin Sokoto da Kano da Zamfara da Bauchi da Ebonyi da Enugu da Abia da Akwa Ibom daga yau zuwa Juma’a.

A gefe guda kuma, za a iya fuskantar matsakaicin ruwan sama a yankunan jihohin Rivers da Kwara da Delta da birnin Abuja da arewacin Kaduna.

Hukumar ta yi gargadin cewa sakamakon hasashen ruwan sama kamar da bakin kwarya da za a samu cikin kwana uku masu zuwa, akwai yiwuwar a samu ambaliyar ruwa a kan tituna da gidajen da ke cikin kwari da koramu da kuma koguna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: