Kamar yadda BBCHausa ta wallafa, “Al’ummar Anambra a kudancin Najeriya na shirin zaɓen sabon gwamnan jihar

Hukumar zaɓe mai zaman kanta Inec ta ce misalin ƙarfe 8:30 na safe za a fara zaɓe a kammala ƙarfe 2:30 na yamma.

Inec ta ce ƴan takara daga jam’iyyun siyasa 18 ne za su fafata a zaɓen da suka ƙunshi na manyan jam’iyyun siyaaa guda biyu na Najeriya PDP da APC.

Mutum miliyan biyu da rabi ke da ƴancin kaɗa ƙuri’a a runfunan zaɓe 5,720 a jihar. Sai dai kuma kawai wasu wauraren da ba za a yi zaɓen ba saboda babu waɗanda suka yi rijista.”

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: