Ambaliya a ƙasashen yammacin Afirka ta yi sanadin raba mutum kusan 950,000 da muhallinsu

675

Kungiyar kare haƙƙin yara ta Save the Children ta ce ambaliya a ƙasashen yammacin Afirka ta yi sanadin raba mutum kusan 950,000 da muhallinsu tare da hana yara samun ilimi.

Rahoton ƙungiyar ya ce kusan mutum 649,184 ambaliyar ta raba da gidajensu a Nijar, yayin da a Najeriya kuma ta raba mutum 225,000 da gidajensu.

Ambaliyar ta kuma raba mutum 73,778 da muhallinsu a kasar Mali, a cewar Save the Children.

Hukumomin Najeriya sun ce ambaliyar ta shafi jihohi 29 cikin 36 na ƙasar, galibi a arewacin ƙasar inda ta yi sanadin mutuwar mutum kusan 200.

Ambaliyar ta kuma shafe gonaki da dama tare da tafiya da gidaje da dabbobi.

Comments are closed.

hitta mer om recensioner