Ambaliyar ruwan sama ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 68 a Kano da Jigawa

0 187

Akalla mutane 68 ne aka ruwaito sun rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da aka samu a jihohin Kano da Jigawa tun farkon damina a watan Yuli.

Da yake bayyana adadin wadanda suka mutu, babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano SEMA, Isyaku Kubarachi ya ce adadin wadanda suka mutu a jihar ya kai 31. 

Isyaku wanda ya tabbatar da hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano, ya ce ambaliyar da ta shafi al’ummomi kusan 156 a fadin kananan hukumomi 21 na jihar ya kuma yi sanadiyyar jikkata mutane 135,da kuma lalata gidaje dubu 5,280 yayin da mutane 313 suka rasa matsugunansu.

A nan jihar jigawa kuma, Sakataren zartarwa na Hukumar Bada Agajin Gaggawa na Jihar, Dokta Haruna Mairiga ya ce adadin wadanda suka mutu sakamakon mamakon ruwan sama da ya haddasa ambaliyar ruwa ya kai 37 a jihar.

Dr. Mairiga ya ce ambaliyar ta kuma raba mutane dubu 15,000 da muhallansu yayin da hekta dubu 12,000 na gonakin da aka noma ya lalace.

Ya ce ambaliyar ta shafi kananan hukumomi 17 daga cikin kananan hukumomi 27 da ke cikin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: