Babban Banki na Najeriya CBN ya rage kuɗin da bankuna ke cazar ‘yan Najeriya kan turawa da cirar kuɗi

Babban Bankin Najeriya CBN ya ba da umarnin rage kuɗin da bankunan ƙasar ke caza yayin cire kuɗi ta ATM da kuma tura kuɗin ta intanet tsakanin bankuna.

Matakin na ƙunshe ne cikin wata sanarawa da Chibuzor Efobi, shugaban sashen kula da tsare-tsaren kuɗi da dokoki, ya fitar yana mai umartar bankuna da cibiyoyin kudi da su sauya tsarin cazar ‘yan Najeriya.

CBN ya ce an ɗauki matakin ne saboda a tabattar bankunan na bin sabbin tsarin da kasuwanci ke tattare da shi.

Sauyin ya shafi N65 da ake cazar mutum idan ya ciri kuɗi ta ATM na bankin da ba nasa ba sau uku cikin wata ɗaya, inda aka mayar da shi N35.

Haka nan kuma an rage cajin aika kudi ta intanet tsakanin bankuna daga N300 zuwa N50 a matsayin mafi yawan adadin da za a caji mutum.

A cewar sanarwar, kazalika akwai tsarin bin diddigin ayyukan bankunan don tabbatar da cewa an daƙile yawan cazar mutane ba tare da amincewarsu ba.

Comments (0)
Add Comment