Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sakin zunzurutun kudi har Naira Biliyan Goma N10b domin yin aikin ƙidayar jama’ar kasar nan.
Kuɗaɗen dai za a sakarwa hukumar ƙidaya ta ƙasa (NPC) domin cigaba da ɗaukar alkaluman yankuna da kananan hukumomi 546 na ƙasar nan.
- Burkina Faso ta dakatar da wasu kafafen watsa labarai da dama na Ƙasashen Yamma har sai baba ta gani
- Karyewar gada ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 24 a lardin Guangdong na kudancin kasar China
- Isra’ila na dab da fara kai hare-hare birnin Rafah na kudancin Gaza ta ƙasa – Martin Griffiths
- Gwamnonin jahohin arewa sun bayyana damuwa bisa cigaba da karuwar rashin tsaro a shiyyar
- Gwamnatin Tarayya ta shirya tsaf domin bayar da cikakkiyar dama ga matatar man fetur ta Dangote
Muƙaddashin Shugaban hukumar Dr. Eyitayo Oyetunji ne ya shaidawa manema labarai hakan a shalkwatar hukumar.
A cewarsa, shugaba Buhari ya kuma amince da sakin wasu karin Naira NE.5b domin sakawa cikin kasafin 2021 don kammala wasu aiyukan da ake yi a yunkurin shirye-shiryen ƙidayar da za a gudanar nan gaba.