An ƙara farashin Fetur zuwa 143.80

0 310

Shashin dake kula da kayyade farashin fetur na kasa PPPRA ne ya sanar da hakan a wata sanarwar da babban sakatarenta Abdulkadir Sa’idu ya fitar yau Laraba.

Ya ce “Bayan duba kan farashin man a cikin watan Yuni da kuma la’akari da bukatar kasuwar domin cigabanta, muna masu bayar da shawarar daga farashin man daga N140.80 zuwa N143.80 duk lita guda”.

A cikin watan Afrilu ne dai idan ba’a manta ba gwamnatin ta sanar da rage farashin fetur zuwa N123.50 lita.

Abin jira a gani dai shi ne ko dillalan man fetur din zasu jira tsohon kayansu mai tsohon farashi ya kare kafin su dauko sabon kaya a sabon fara ko kuma zasu daga farashin nan take.

Leave a Reply

%d bloggers like this: