An Aika Da Jami’an ‘Yansanda Kan Titunan Nairobi Gabannin Zanga-Zangar ‘Yan Adawa

0 171

An aika da jami’an ‘yansanda kan titunan Nairobi, babban birnin kasar Kenya, gabannin zanga-zangar da ‘yan adawa suka shirya gudanarwa.

Jagoran ‘yan adawa, Raila Odinga, ya sha alwashin dawowa zanga-zangar duk da gargadin da hukumomin suka yin a cewar baza su bari a gudanar da it aba, domin kula da tsaron kasa, tare da bayar da misalai na tashin hankali a zanga-zangar baya.

Amma Raila Odinga ya kafe kan cewa za a fara zanga-zangar a yau kuma yace zanga-zangar za ta zama ta lumana bisa tandadin kundin tsarin mulki.

Yace babu yadda za ayi ‘yansanda su yanke hukuncin haramta zanga-zangar bisa hujjar cewa za ayi tashin hankali, duk da kundin tsarin mulki ya bayar da damar zanga-zanga.

Dokokin kasar Kenya sun tanadi halascin gudanar da zanga-zanga kuma ba tare da amincewar ‘yansanda ba.

Tunda farko a safiyar yau, cibiyar kasuwancin birnin ta kasance cikin kwanciyar hankali inda mutane ke gudanar da harkokinsu, duk da kasancewar akwai ‘yansanda masu yawa kan wasu tituna.

Leave a Reply