An ayyana dokar ta-ɓaci bayan ɓarkewar cutar kwalara a Zimbabwe

0 286

Zimbabwe ta ayyana dokar ta-ɓaci bayan ɓarkewar cutar kwalara a Harare, babban birnin ƙasar.

Ɓarkewar cutar ta janyo mutuwar gomman mutane da kuma 7,000 waɗanda ake tunanin sun kamu da cutar.

Hukumomin birnin sun ce ɓarkewar cutar, wadda kuma ke yaɗuwa cikin birnin, ta tuno da irin mummunan cutar da ta ɓarke a shekarar 2008, inda dubban mutane suka mutu.

Kafofin yaɗa labara a birnin sun ruwaito magajin birnin, Ian Makone na cewa, “Mun ayyana dokar ta-ɓaci saboda ɓarkewar kwalara.

A yanzu hukumomi na yin kira domin a taimaka wajen daƙile yaɗuwar cutar da samar da tsaftataccen ruwa, inda suka ce agajin da ake bayar ya yi kaɗan.

Hukumomin lafiya na can suna ta ƙoƙarin ganin sun dakile yaɗuwar cutar domin rage yawan mutanen da ake kwantarwa a asibiti bayan ɓarkewar cutar, a cewar hukumar bayar da agaji ta IFRC.

Biranen Zimbabwe dai sun yi ta fuskantar matsalar isassun likitoci da zu taimaka wajen shawo kan masu kamuwa da cutar, da kuma rashin magunguna.

Ƙasar ta yi ta fama wajen yaƙi da ɓarkewar kwalara a baya-bayan nan a daidai lokacin da ake fuskantar ƙarancin tsaftataccen ruwa.

Garin Kuwadzana da ke Harare, ya kasance wajen da masu fama da cutar suka fi yawa, inda kusan rabin al’umma garin suka kamu, kamar yadda alƙaluma suka nuna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: