An bada umarnin sakin jami’ar sojan da ta amince da tayin soyyayar da wani matashin mai hidimtawa kasa (NYSC) yayi a gareta

0 101

Babban hafsan sojin kasar nan laptanal ganar Faruk Yahaya ya bada umarnin sakin jamiar sojan nan wacce ta amince da tayin soyyayar da wani matashin mai hidimtawa kasa wato NYSC yayi a gareta a sansanin horas da matasan dake Yikpata a jihar kwara..

An tattaro cewa shugaban sojin ya bada umarnin gaggawa kan sakin sojan wacce aka yiwa afuwa albarkacin ranar bikin kirsimeti ta bana.

Farouk yahya ya bukaci jami’ar sojan da kasance mai biyyaya ga dokokin hukumar soji, tare kauracewa dukkanin ayyukan rashin ji.

A makonnin baya ne Manema labarai suka rawaito yadda matsashin saurayin mai hidimtawa kasa yayi wa jamiar wacce aka bayyana sunan ta da Sofiyat Akanlabi sojin tayin soyayya.

Tsare jamiar ya ya sanya wani lauyan kare hakkin dan adam, ya zargi sojojin da take hakkin sojan.

Kawo yanzu Kakakin rundunar, Brigediya Genar Onyema Nwachukwu, baice komai ba dangane da lamarin, sai dai manema labarai sun tuntubeshi domin jin ta bakinsa, amma An kasa samun sa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: