An buɗe rumfunan zaɓe 326 a Karamar Hukumar Ihiala ta jihar Anambra domin kammala zaben gwamna da aka yi a karshen mako

0 145

An buɗe rumfunan zaɓe 326 a Karamar Hukumar Ihiala ta jihar Anambra, domin kammala zaben gwamna da aka yi a karshen mako.

Jami’ar tattara sakamaon zaɓe, Farfesa Florence Banku Obi ta dakatar da aikin bayyana dan takarar da ya yi nasara a zaɓen gwamnan na jihar Anambara na ranar Asabar.

Har sai an kammala zaɓen ƙaramar hukumar Ihiala, wanda hukumar zaben INEC, ta gaza yi saboda wasu dalilai ciki har da batun tsaro, kamar yadda ta ce.

Sakamakon da ta rigaya ta sanar a ranar Lahadi ya nuna cewa ɗan takarar jam’iyyar APGA, Farfesa Charles Soludo ne ke kan gaba da ƙananan hukumomi guda 18.

Sai Mista Valentine Ozigbo na jam’iyyar PDP da ya samu ƙaramar hukuma ɗaya, yayin da Sanata Ifeanyi Ubah na Jam’iyar YPP ya samu ƙaramar hukuma ɗaya.

A ranar Lahadi ake sa ran za a sanar da sakamakon zaben baki daya da dan takarar da ya yi nasara, to amma hakan ba ta samu ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: