An bude shafin internet na neman shiga aikin sojan Najeriya ga masu sha’awa.

An bude shafin na internet domin daukar kananan sojoji mata da maza karo na 83.

An bude shafin a jiya kuma zai kasance a bude har zuwa ranar 13 ga watan Maris da muke ciki.

Ana sa ran wadanda ke neman aikin su kasance basu da aure kuma cikakkun ‘yan Najeriya, sannan dole ya zama suna da katin shaidar zama dan kasa or number shaidar asusun banki ta BVN.

Kazalika ya kasance suna da cikakkiyar lafiyar jiki da ta kwakwalwa, bisa tanadin dokokin hukumar sojin Najeriya.

Ga duk mai bukata, dole ya zama yana da pass akalla 4 a jarabawa 1 ko 2 ta kammala makarantar sakandire.

Haka kuma wanda zai nemi aikin kada yayi kasa da shekaru 18 kuma kada ya haura shekaru 22,

Kazalika, an bayar da rahotan cewa zuwa ranar 8 ga watan Augusta bana ne za a fara bayar da horo.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: