An ceci mutane 154 da kadarori na Naira miliyan 80 daga aukuwar gobara a jihar Kano

0 154

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce ta ceci mutane 154 da kadarori da darajar kuɗinsu ya kai naira miliyan 80 daga aukuwar gobara 13 daban-daban a watan Yuli.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Alhaji Saminu Abdullahi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai jiya Litinin a Kano.

Abdullahi, ya ce duk da wannan namijin ƙoƙari kimanin mutane 150 da dabbobi da dama ne suka mutu sakamakon gobarar da aka yi a tsawon lokacin.

Ya shawarci jama’a da su riƙa kula da wuta tare da tabbatar da sun kashe duk wata na’urar lantarki kafin barin wuraren da suke aiki ko harkokinsu na kasuwanci, musamman masu dafa abinci da sayar da abincin dare.

Ya kuma buƙaci masu ababen hawa da su yi taka-tsan-tsan a lokacin damina domin guje wa abubuwan da ka iya aukuwa wanda ba a sani ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: