An ceto wani dattijo dan shekara 60 wanda ya makale a rijiya a jihar Kano

0 82

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ceto wani dattijo dan shekara 60, mai suna Adamu Manjo da ya makale a rijiya a unguwar Dandishe dake karamar hukumar Dala ta jihar.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Saminu Abdullahi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu kuma ya rabawa manema labarai jiya a Kano.

Saminu Abdullahi ya bayyana a cikin sanarwar cewa lamarin ya faru ne da safiyar jiya.

Ya ce wani mutum ne mai suna Abubakar Shehu-Musa ne ya dauki Adamu Manjo aiki domin ya hako masa yashi amma sai ya makale cikin rijiyar.

Saminu Abdullahi ya kara da cewa an fito da wanda abin ya rutsa da shi daga rijiya da rai kuma an mika shi ga Abubakar Shehu-Musa mazaunin unguwar ta Dandishe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: