An dakatar da shari’ar Sheikh Abduljabbar Kabara saboda rashin lafiyar alkalin kotun

0 60

An dakatar da shari’ar Sheikh Abduljabbar Kabara saboda rashin lafiyar alkalin kotun, Ibrahim Sarki-Yola na Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kano.

Gwamnatin jihar Kano ta tuhumi Abduljabbar Kabara da laifuka guda hudu da suka hada da kalaman batanci ga Annabi Muhammad SAW.

A zaman da aka ci gaba da shari’ar, jami’in hulda da jama’a na kotun daukaka karar shari’ar Musulunci ta Jihar Kano, Malam Muzammil Ado-Fagge, ya shaida wa manema labarai a yau cewa an dakatar da shari’ar ne saboda rashin lafiyar alkalin kotun.

Idan ba a manta ba a ranar 12 ga watan Mayu ne kotun ta umurci Majalisar Agajin Shariah ta kasa da ta bayar da lauya ga Abduljabbar Kabara a shari’ar batanci da ake yi.

Tun da farko, lauyan masu shigar da kara, Suraj Sa’eda, ya yi zargin cewa wanda ake tuhumar ya yi kalaman batanci ga Annabi Muhammad SAW a aurensa da Nana Safiyya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: