An damƙe wasu kan badaƙalar sayar da fam ɗin aiki a ofishin shugaban ma’aikatan jihar Kano

0 123

Hukumar karɓar korafe-korafen jama’a da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ta damƙe wasu mutane biyu tare da gayyatar wasu sakatarori guda uku, domin amsa tambayoyi kan badaƙalar sayar da fam ɗin aiki a ofishin shugaban ma’aikata.

Shugaban hukumar Muhuyi Rimin-Gado ne ya bayyana hakan a Kano, inda ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin ganowa rate da gurfanar da waɗanda ke da hannu a badaƙalar zambar da ta shafi dubban masu neman aiki.

Muhyi ya ci gaba da cewa, a binciken farko da aka gudanar an gano wasu ayyukan damfara a ofishin shugaban ma’aikata da hukumar kula da makarantun sakandire ta jihar Kano da ta kula da ma’aikatan lafiya.

A cewarsa, binciken da ake yi zai fallasa tare da gurfanar da waɗanda suke damfara wajen sayar da fam ɗin aikin, kamar yadda gwamnatin jihar ta ba da umarnin yin bincike sosai kan lamarin tare da gurfanar da waɗanda aka samu da hannu a gaban kuliya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: