An fara aiwatar da shirin kula da lafiyar masu karamin karfi a asibitoci 65 dake dasu a jihar Jigawa

0 74

Hukumar Asusun Kiwon lafiya na jihar Jigawa ya fara aiwatar da shirin kula da lafiyar masu karamin karfi na gwamnatin tarayya a kananan asibitoci 65 dake dasu  fadin jihar nan.

Sakataren Zartarwa na Asusun Dr Nura Ibrahim ya sanar da hakan ga manema labarai a Dutse babban birnin Jiha.

A cewarsa, ana aiwatar da shirin ne a cibiyoyin lafiyar dake kananan hukumomi tara daga cikin 27 da ake dasu.

Dr Nura Ibrahim ya kara da cewar a watan gobe ne suke sa ran za a fadada shirin zuwa dukkanin asibitoci 279 da aka zaba domin aiwatar da shirin a mazabun jihar nan 287.

Shugaban Hukumar yace sun gudanar da taron bita ga jami’an kula da asibitocin 279 da manajojin hukumar lafiya matakin farko na kananan hukumomi kan yadda shirin zai samu nasarar da ake bukata.

Dr Nura Ibrahim ya kara da cewar tuni gwamnatin tarayya da hannun hukumar bada kudaden aiwatar da shirin a jihar nan wanda aka fara shirin na gwaji a kananan hukumomi tara na jihar nan.

Kazalika yace hukumar ta bada takardar yabo ga shugaban asibitin Sule tankarkar bisa yin cikakken amfani da kudaden wajen kawata asibitin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: