An gano sassan jikin jariri da aka sassara jikinsa a garin Wudil na jihar Kano.

Mazauna unguwar Sakau da ke Sabon-Garin Wudil sun ce sun wayi gari da ganin gawar jaririn da aka yiwa gunduwa-gunduwa, inda suka ce an samu kafafuwa da kan jariri a gurare daban-daban a cikin ciyayi da bishiyoyi amma ba a samu sauran sassan jikin ba tukuna.

Mai unguwar Sakau, Malam Muhammadu Sule, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce sun sanar da hukumomin da abin ya shafa da ‘yan sanda don gudanar da bincike.

Muhammad Sule ya kuma ce an kai kan jaririn da kafarsa zuwa asibitin Wudil don binciken gawarwaki inda likita ya tabbatar da cewa an daddatsa jaririn inda aka yi masa gunduwa-gunduwa.

Hakimin Sabon Garin Wudil, Garba Me Disai, wanda shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bukaci mazauna yankin da su kasance masu taka tsan-tsan, su kuma su kai rahoton duk wani abin da ake zargi a yankunan su ga hukumomin da abin ya shafa don daukar matakan da suka dace.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: