Gwamnatin tarayya ta ce gano Alakar mai karfi tsakanin mai kokarin kafa daular kasar Yarabawa wato Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho da kuma ayyukan ta’addanci.

Ministan Ma’aikatar Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnati Abubakar Malami SAN, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake yiwa manema labarai Jawabi a Abuja.

A cewarsa, gwamnatin tarayya ta samu rahoton kan yadda Sunday Igboho ya ke samun kudade a wani Kamfani mai suna Adesun International Concept Limited wanda aka yiwa rijista a watan Afrilu na shekarar 2010.

Abubakar Malami, ya ce Kamfanin yana da mutane 2 masu suna Oladele Oyetunji da Aderopo Adeyemo, a matsayin Daraktoci kuma Kamfanin yana da Asusun 43 a bankuna 9.

Haka kuma ya ce wani Dan Majalisar Kasa ne yafi kowa turawa Kamfanin na Sunday Igboho kudade, inda yake kimanin Naira Miliyan 127 da dubu 145 ne aka turawa Kamfanin tun daga ranar 22 ga watan Octoba na shekarar 2013 zuwa ranar 28 ga watan Satumba na shekarar 2020.

Kazalika, Ministan ya ce bincike ya gano alakar da take tsakanin Kamfanin Sunday Igboho da kuma Kamfanonin gine-gine da wasu yan kasuwa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: