Hukumar tsaron fararen hula Civil Defence ta gano wani jariri da aka jefar a cikin sokawe na bandaki a unguwar Kwarin Manu da ke karamar hukumar Hadejia.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar a jiha, Adamu Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a birnin Dutse.

Ya ce lamarin ya faru ne a jiya bayan Umar Muhammad mai shekaru 47 ya kai rahoto ga hukumar cewa ya hangi wani abu a bandakinsa.

Adamu Shehu ya ce, jami’an Civil Defence garzaya wajen da lamarin ya faru kuma an gano gawar jariri daure a jikin rigar matashin kai a cikin sokawe na bandakin.

Adamu Shehu ya ce, Umar Muhammad yana hannun hukumar ta civil defense wacce ta tsare shi don yi masa tambayoyi.

Ya ce an dauke gawar kuma an kai ta Babban Asibitin Hadejia inda aka tabbatar da mutuwar jaririn.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: