An Gano Wani Yaro Daya Bata Dan Asalin Jihar Kano Mai Shekaru 14 A Jamhuriyar Togo

0 88

An gano wani yaro a jamhuriyar Togo, dan shekara 14 dan unguwar Hotoro da ke Kano a jihar Kano, wanda iyayensa suka bayyana bacewarsa a wani lokaci cikin watan Maris.

A cewar wani shirin gidan rediyon Freedom wanda Editan mu ya saurara, an gano yaron ne tare da wani yaro, shi ma dan Najeriya, suna yawo a kan titi a kasar Togo, suna barar abinci.

An ce an same su ne ta hanyar wata shahararriyar ‘yar Najeriya da ke sayar da abinci a kasar Togo, Hajiya Maijidda Mai Abinci, wadda ta ce wasu mutane ne suka kawo su domin sun ce su ‘yan Najeriya ne.

Ta ce yanzu haka an ajiye su a kasar Togo a wajenta, kuma ta yanke shawarar tuntubar ‘yan Najeriya domin neman iyayensu. Mahaifin yaron ya yabawa Hajiya Maijidda Mai Abinci kuma ya roki jama’a da su taimaka masa domin ba shi da kudin tafiya kasar Togo domin ya dauko dansa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: