An gayyaci matar da ta yayyaga fasfo ɗin mijinta a filin jirgin sama na Legas

0 146

Hukumar kula da shige da fice a kasarnan ta gayyaci wata mata domin amsa tambayoyi bayan an gan ta a wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta tana yayyaga fasfo ɗin mijinta a filin jirgin sama na Legas.

Matar mai suna Favour Igiebor, an gan ta a cikin bidiyon tana yi masa ihu tare da watsar da takardun fasfo ɗin a ƙasa.

Ta dawo daga Turai ne tare da mijinta da ‘ya’yanta, wadanda suka sauka a filin jirgin sama na Murtala Mohammed, inda lamarin ya faru a gaban waɗansu fasinjojin.

“Hukumar kula da shige da fice ta Najeriya ta soma gudanar da bincike kan wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda wata fasinja ta yayyaga fasfo ɗin mijinta a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas,” in ji wata sanarwa daga hukumar.

“Mun gano matar, sunanta Mrs. Favour Igiebor,” a cewar hukumar.

Hukumomin ƙasarnan sun ce laifi ne a kekketa fasfo ɗin kuma duk wanda aka kama da laifi zai iya shafe shekara guda a gidan yari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: