An gudanar da taron kwanaki 2 ga masu amfani da jiragen ruwa domin kawo karshen kifewar jirgi

0 92

Hukumar kula da hanyoyin ruwa (NIWA) ta gudanar da taron kwanaki biyu ga masu ruwa da tsaki da ke amfani da jiragen ruwa a ranar 24 zuwa 25 ga watan Agusta, 2024, domin magance matsalar yawan samun ambaliyar ruwa, da wayar da kan masu ruwa da tsaki, da kuma fasinjojin masu amfani da jirgin ruwa a matsayin hanyar zirga zirga a jihar Kebbi musamman mutanen da ke kusa da gaɓar Kogi.

Taron wanda ya samu halartar wakilai daga mai martaba Sarkin Yauri, da HYPPAD, , da sauran hukumomin tabbatar da tsaro.

Taron dai ya mayar da hankali ne kan illolin da ke tattare da ambaliyar ruwa da kuma muhimmancin bin ƙa’idojin kariya yayin amfani da jiragen ruwa,

A ɓangaren Fasinjoji tattaunawar ta ta’allaka ne kan matakan kariya na wajibi, da sanya rigunan kare nutsewa kafin shiga kwale-kwale, hana tafiye-tafiye cikin dare, samun na’urorin kashe gobara a cikin jirgi da kuma wuce ƙa’idar lodin kaya ko fasinjojin don hana kifewar jirgi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: