Alƙaliyar Alƙalai ta Jihar Zamfara Mai Shari’a Kulu Aliyu ta rantsar da kwamatin mutum biyar da zai binciki laifukan da ake zargin Mataimakin Gwamna Mahdi Aliyu Gusau na rashin ɗa’a.

Kwamatin ƙarƙashin tsohon Alƙali Tanko Soba, an kafa shi ne sakamakon damar da kundin tsarin mulki ya ba wa alƙaliyar, a cewar Mai Shari’a Kulu.

Ta ƙara da cewa Sashe na 185(5) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ne ya ba ta damar kafa kwamatin sakamakon buƙatar da Majalisar Dokokin Zamfara ta gabatar mata ranar 10 ga watan Fabarairu ta ƙorafi kan mataimakin gwamnan.

BBCHausa

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: