An Harbe Wani dan Sanda Da Ke Bakin Aiki A Jihar Oyo

0 74

Wasu ‘yan bindiga sun harbe wani dan sanda da ke bakin aiki a ofishin ‘yan sanda ta Moniya da ke Ibadan a jihar Oyo, yayin da yake bin sawun wasu da ake zargi da aikata laifuka a Ibadan.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa ya rawaito cewa lamarin ya faru ne a tashar mota ta Moniya da ke karamar hukumar Akinyele a jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Adewale Osifeso, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Ibadan.

A wani labarin kuma, rahotanni sun ce an yi garkuwa da wani limamin cocin Katolika da ba a bayyana sunan sa ba a shatale-talen Nnobi da ke karamar hukumar Idemili ta Kudu a jihar Anambra.

Wani ganau ya ce mutumin da ke cikin mota kirar Lexus na kan hanyar Awka-Etiti ne a lokacin da ‘yan bindigar suka yi masa dirar mikiya.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, Ikenga Tochukwu, ya ce ba a kai rahoton lamarin ga ofishin sa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: