An harbe wani gawurtaccen dan fashin daji kuma jigo a satar shanu a jihar Zamfara

0 132

An harbe wani gawurtaccen dan fashin daji kuma jigo a satar shanu a jihar Zamfara, mai suna Damina.

Marigayin yana da sansani a dajin Kuyanbana da ke masarautar Dansadau ta karamar hukumar Maru.

An kashe Damina ne a wata arangama da kungiyar da Dogo Gide ke jagoranta.

An rawaito cewa dan bindigan da aka kashe ya kasance yana da hannu wajen kai munanan hare-hare da garkuwa da mutane da satar shanu da kuma sanya haraji kan wasu al’ummomi a masarautar Dansadau ta jihar.

A watan Yulin da ya gabata ne Damina ya kai hari a kauyukan Tungar Baushe da Randa, inda aka kashe mutane da dama tare da yin garkuwa da wasu mazauna yankin fiye da 100, galibinsu mata da kananan yara.

Majiyoyi sun shaidawa manema labarai cewa Damina ya mutu ne sakamakon munanan raunukan da ya samu biyo bayan wani kazamin artabu tsakanin ‘yan kungiyarsa da ‘yan kungiyar Dogo Gide.

Leave a Reply

%d bloggers like this: