An kaddamar da shirin koyar da sana’oin dogaro da kai ga mata 100 a jihar Jigawa

0 179

Ma’aikatar lura da al’amuran mata da walwala jama’a ta jihar Jigawa ta kaddamar da shirin koyar da sana’ion dogaro da kai ga mata dari daya a cibiyar bunkasa al’amuran mata dake Dutse.

A jawabin da ta gabatar a lokacin taron bude shirin koyar da sana’oin, mai dakin gwamnan jiha Hajiya Hadiza Umar Namadi ta ce gwamnatin jiha ta sa himma wajen baiwa mata kulawa ta musamman.

Hajiya Hadiza Umar Namadi ta kara da cewa gwamnatin jiha na baiwa yaya mata ilimi kyauta tun daga firamare zuwa jami’a  tare da samar  da magunguna kyauta ga yara yan kasa da shekara biyar da kuma sanya mata cikin harkokin gwamnati a matakai daban-daban.

Mai dakin gwamnan ta kuma bukaci Matan da za;a koyawa sana’oin su maida hankali kan abubuwan da zasu koya domin su zama masu dogaro da kan su .

Tun farko a jawabinta kwamishiniyar ma’aikatar al’amuran mata da walwalar jama’a  ta jihar Jigawa Hajiya Hadiza T. Abdulwahab ta ce za’a koyawa mata sana’oin yin sabulu da yin takalma da jaka da sauran su.

Hajiya Hadiza T. Abdulwahab ta ce za’a dauki tsawon watanni biyu wajen koyar da su wadannan sana’oi,  inda ta kara da cewa ma’aikatar ta gudanar da ayyuka masu yawa a bangarori daba-daban cikin shekara guda da gwamna Malam Umar Namadi yayi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: