An kaddamar da wata sabuwar kungiyar tsaron gari a garin Kwalam dake jihar jigawa

0 131

Alummar garin Kwalam dake karamar Hukumar Taura sun kaddamar da wata sabuwar kungiyar tsaron gari mai suna Kwalam concerned association domin dakile barazanar tsaro da munanan dabi’u musamman daga matasa

A jawabinsa wajen kaddamar da kungiyar, sabon shugaban kungiyar kuma tsohan sakataren KH Taura Alhaji Lawan Shuaibu Kwalam ya ce alummar garin Kwalam an sansu da hadin kai , da taimakon juna da rikon amana da neman Ilmi da dogaro da kai amma abin takaici a wannan lokaci wadannan halaye sun yi karanci

Saboda sakaci daga Iyaye da taamula da abubuwan sa maye daga matasa wadda ya jefa su cikin sace sace na dukiyoyin mutane

Lawan Shuaibu Kwalam ya ce domin dakile wadannan munanan dabiu ya sa aka kafa wannan kungiya wacce take samun hadin kai daga rundunar yansanda ta jiha da sauran jamian tsaro da masana sharia da suka fito mata da dokokinta dan samun nasarar manufofinta

Ya ce burin kungiyar bashi bane na hukunta masu aikata irin wadannan miyagun laifuka, illa kawai matasa masu aikata hakan su daina

A jawabinsa , mai baiwa gwamna shawara kan makarantun tsangaya Malam Mujitafa Sale Kwalam  ya danganta irin wannan hallaya ta matasa ga rashin neman ilmi da kokarin yin sana-ar dogaro da kai.

Hakimin Kwalam Magajin Malam na Ringim Alhaji Muttakah Uma ya ce sakacin rashin tsaron dukiyar alumma a garin kwalam, ba daga iyaye ne kawai ba, laifin na kowa da kowa ne, inda yace ko dansa aka kama da laifin aikata mumunan dabia akama shi a hukuntashi

Tuni dai kungiyar ta Kwalam concerned association ta fito da dabarun yaki da munanan halaye a garin data kira operation ruwan sama da operation zaman lafiya dole

Barista Muhammad Lawan Kwalam ya karanto tare da yin bayani kan dokokin kungiyar , inda ya ce bisa doka ba a yarda da zirga zirga a garin Kwalam daga karfe 11 na dare zuwa 6 na safe

Taron ya samu halartar baturen yansanda na karamar hukumar Taura DPO Adamu Muhammad Danjuma da sauran manyan baki

Leave a Reply

%d bloggers like this: