An kama ɗan ta’addan da ake zargi da kitsa harin da aka kai a ƙauyen Mararaban Azagawa da ke ƙaramar hukumar Bali a jihar Taraba

0 141

A wani gagarumin samame da suka kai, dakarun rundunar 6 sun kama ɗan ta’addan da ake zargi da kitsa harin da aka kai a ƙauyen Mararaban Azagawa da ke ƙaramar hukumar Bali a jihar Taraba.

Rundunar ta ce kamen ya biyo bayan harin da aka kai ranar 16 ga watan Yunin 2024, wanda ya yi sanadin asarar rayuka biyar da jikkata mutane da dama.

Muƙaddashin Daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta 6, Oni Olubodunde ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.

A cewarsa, dakarun da ke sansanin ‘Forward Operating Base’ a ƙaramar hukumar Bali, sun ƙaddamar da wani samame na musamman bayan sahihan bayanan sirri da suka samu domin kamo waɗanda suka kai harin.

A yayin samamen ne sojojin suka kama wanda ake zargin shi ne ya kitsa harin mai suna Hassan Ibrahim wanda aka fi sani da Godu, ɗan shekara 39, kamar dai yadda sanarwar ta ce.

Leave a Reply

%d bloggers like this: