An kama daya daga cikin mutane hudu da suka tsere wadanda ake zargi a kisan kare dangi na kasar Rwanda a shekarar 1994.
Masu gabatar da kara na Majalisar Dinkin Duniya sun ce an kama Fulgence Kayishema a kasar Afirka ta Kudu kuma ana sa ran zai fuskanci shari’a a Rwanda.
An tuhumi tsohon sufeton ‘yan sandan ne a shekara ta 2001 kan wani lamari da ya faru a lokacin da aka kashe maza da mata da yara ‘yan kabilar Tutsi sama da dubu biyu a cikin wata cocin Katolika da suka nemi mafaka.
An kashe ‘yan kabilar Tutsi da ‘yan kabilar Hutu masu matsakaicin ra’ayi kimanin dubu 800 a kisan kiyashin.
A cewar tuhumar, ana zargin Fulgence Kayishema da tsarawa da aiwatar da kisan gillar wasu mutane dake neman mafaka a cocin a ranar 15 ga Afrilun shekarar 1994.
Daga nan aka binne gawarwakinsu a cikin manyan kaburbura.