An kama gawurtattun waƴanda suka sace ɗan’uwan Sarkin jihar Taraba da kuma kashe wani jami’in kwastam

0 100

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kama wasu da ta kira gawurtattun masu garkuwa da mutane 11 a Jihar Taraba da ke tsakiyar Najeriya tare da ƙwace makaamai da dama.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar a yau Lahadi ta ce mutanen suna da hannu a hare-hare da dama, ciki har da satar wani jami’in hukumar kwastam da wani ɗan uwan sarkin Jalingo da kuma ɗan sanda mai muƙamin saja duka a Jalingo, babban birnin jihar.

Kakakin ‘yan sanda Frank Mba ya ce dakarunsu sun yi nasarar ƙwace bindiga tara jumilla, ciki har da AK-47 bakwai, da ɗumbin harsasai da ƙwayoyi da takunkumi yayin samamen da suka kai.

“Kamen waɗanda ake zargin ya biyo bayan tura rundunar gaggawa ta Intelligence Response Team zuwa Taraba domin taimaka wa ‘yan sandan Taraba wajen kawo ƙarshen satar mutane cikin gaggawa,” in ji Frank Mba.

Kazalika, sanarwar ta zargi biyu daga cikin mutanen da hannu wajen kashe wani ɗan sanda da kuma raunata wani yayin wani hari da suka kai, inda suka yi garkuwa da wasu mutane.

Source: BBCHausa

Leave a Reply

%d bloggers like this: