Hukumar Hisba a Jihar Jigawa ta ce ta kama kwalaben giya dubu 1 da 906 a ayyukan ta daban-daban a jihar nan a shekarar 2021.

Kwamndan Hisbah na jiha Malam Ibrahim Dahiru ne ya bayyana hakan a yau yayin ganawa da manema labarai a Dutse.

Malam Dahiru ya kara da cewa an kama kwalaban giyar ne yayin sumame da suka kai mashaya daban-daban tare da otal-otal dake jihar nan.

Yace an kama mutane 92 da ake zargi ciki har da mata masu zaman kansu bisa aikata laifukan rashin da’a.

Malam Dahiru yace shan giya haramun ne ga musulman jihar nan, ya kuma yi kira ga mutane da su guji jefa kansu cikin laifuka rashin da’a da duk wani laifi da zai iya lalata rayuwar al’umma.

Ya kuma kara da cewa an mika wasu kwalaben giyar da kuma wadanda da ake zargi ga hukumar ‘yan sanda domin fuskantar hukunci.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: