An kama mai saida maganin kwari na fesawa amfanin gona na jabu a kasuwar Hadejia

0 84

Kwamatin kare hakin mai saye da mai sayarwa na jihar Jigawa, ya kama wani mutum mai suna Bala Lawan da maganin kwari na fesawa amfanin gona na jabu har katan shida a kasuwar Hadejia.

Shugaban kwamatin na jiha Alhaji Farouk Abdallah Malam Madori ya ce tuni ya gabatar da shi a gaban kotun tafida gidanka karkashin majistirin Munnir Sarki Jahun.

Bayan ya amsa laifinsa kotun ta yanke masa wa’adin zama a gidan maza na tsawon wata shida ko kuma zabin biyan tara naira dubu sittin, kotun kuma ta yanke masa hukuncin daurin talala.

Farouk Abdallah Malammadori ya kuma yi kira ga manoma da su kai rahotan duk mutumin da ya sayar musu da maganin feshi ko taki na jabu ga kwamatinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: